Boko Haram: An kashe mutane a Chibok

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Rahotani daga jihar Borno dake arewacin Nigeria sun ce mutane akala 11 ne aka kashe lokacinda wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari a kauyen Takulashi dake karamar hukumar Chibok.

Rahotanin sun kuma ce maharan su kona gidaje da dama dake kauyen a harin da aka kai a daren ranar Litinin.

Mazauna garin sun shaidawa BBC cewar sun nemi jami'an tsaro a kan su kawo masu dauki lokacin da lamarin ya faru sai dai sun ce babu wani jami'in tsaro ko daya da ya zo har sai da safiyar ranar Talata.

Sai dai a nasu bangaren jami'an tsaron Nigeria sun ce su kan kai dauki a duk lokacin da al'ummomi dake mawuyacin hali suka nemi a kai masu dauki.

A cikin wata sanarwar da kakakin shedkwatar tsaro ta Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade ya ce sojoji sun kaiwa al'ummar dake yankin tafkin Chadi dauki lokacin da suka kirasu ta wayar tarho bayan masu tada kayar dake fama da yunwa suka afkawa yankin.

Karin bayani