JNI ta zargi sojoji da kashe Musulmi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban kungiyar Jama'atu, Sultan Abubakar Sa'ad

Kungiyar Jama'atul Nasril Islam-JNI a Nigeria ta zargi sojojin kasar da kashe Musulmi babu gaira babu dalili a wani matakin da tace tamkar kokarin kawar da musulmin kasar ne.

Kungiyar ta ce sojojin na aikata kisan gilla a kan musulmi da sunan yaki da ta'addanci.

Sakatare Janar na Kungiyar Dr Khalid Aliyu a wata sanarwa, ya zargi jami'an tsaron da kashe Musulmi a jihohin Nassarawa da Yobe da kuma Borno, inda ya bayyana cewar ana neman a kawar da al'ummar musulmi a cikin kasar.

Sai dai a martanin da ta mayar, rundunar tsaron Nigeria ta musanta wannan zargin, inda ta ce kalaman sakatare janar din za su iya tada hankali.

Kakakin rundunar tsaron kasar, Manjo Janar Chris Olukolade a cikin sanarwar, ya ce dakarun kasar za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da son zuciya ba kuma za ta ci gaba da ayyukanta na kawar duk wani abu da zai kawo barazana ga tsaron Nigeria.

Sai dai wanan ba shi ne karon farko da ake zargin sojoji kasar da keta hakin bil'adama ba.

A makon da muke da ciki Hukumar kare hakkin bil'adama ta kasar ta dora alhakin kisan da aka yi wa wasu matasa a unguwar APO dake birnin Abuja a kan sojoji da Jami'an tsaro na farin kaya wato SSS, inda ta umurce su da su biya diyya ta Naira miliyan goma ga iyalan kowanne daga cikin mutane takwas da aka kashe, da kuma Naira miliyan biyar ga ko wanne mutum da ya sami rauni.

Karin bayani