'Apo:Zamu daukaka kara kan biyan diyya'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Nigeria a bakin aiki.

Rundunar tsaron Nigeria ta ce za ta daukaka kara game da hukuncin da aka yanke na biyan diyyar naira miliyan 10 ga iyalan wadanda aka kashe a Apo a birnin Abuja.

Kakakin Rundunar tsaron, Manjo Janar Chris Olukolade ya shaidawa BBC cewar hukuncin abun takaici ne kuma ya nuna bambamci.

Janar Olukolade yace "Akwai yiwuwar zamu daukaka kara, saboda hukuncin ya zarta abunda ya faru. Bayan abunda ya faru kuma ga baki dayan lamarin ya fi karkata kan aikin fafutika wanda ba na ji shi ne babban abunda ke akwai a nan".

Inda ya kara da cewar "To wa kuma zai biya diyar sojin da aka kashe da kuma sauran 'yan Najeriyar da ba su ji ba su gani ba, da 'yan ta'adda suka kashe ko sauran wadanda ta'addanci ya shafa a Najeriya".

A ranar Litinin ne Hukumar kare hakkin bil'adama ta Najeriya, ta ce ta samu rundunar soji da hukumar tsaro ta farin kaya ta SSS da kuma babban lauyan kasar da laifi wajen kisan matasa 8 a unguwar Apo dake Abuja.

Hukumar ta nemi hukumar ta SSS da babban lauyan Najeriya ya biya iyalan mamatan naira miliyan 10 kowannensu, sannan a biya matasa 11 da suka jikkata naira miliyan 5 kowannensu.

Hukumar ta ce babu wata kwakkwarar hujjar dake nuna cewa matasan 'yan Boko Haram ne kamar yadda hukumar SSS din ta fada.

Karin bayani