Samsung ya yi hasashen faduwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Samsung ya yi hasashen cewa gasa za ta zafafa

Kamfanin Samsung, mafi girma wajen kera talabijin da wayoyin salula a duniya, ya yi hasashen faduwar ciniki, watanni shida a jere.

Ribar da ake tsammani ta 8.4 tiriliyan daga watan Janairu zuwa Maris ya ragu, da kashi hudu cikin dari daga wanda kamfanin ya samu a daidai wannan lokaci a bara.

Hakan ya biyo faduwar kashi shida cikin dari da Samsung din ya yi a watannin uku da suka gabace shi.

Faduwar na nuni da cewa kamfanin na fuskantar kalubale na bunkasa kudaden shigarsa, yayin da farashin wayoyin komai da ruwanka ke faduwa.

Rage kudade

Nasarar da kamfanin ya samu wajen sayar da wayoyin komai da ruwanka na Samsung Galaxy ne babban abin da ya bunkasa kamfanin, a 'yan shekarun nan.

Amma kamfanin na fuskantar abokan gasa, bayan wasu kamfanoni suma sun shiga fagen ana dama wa da su.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Abokan hamayya kamar Apple da HTC da wasu kamfanonin China kamar Lenovo, ZTE da Huawei, suma sun nemi hanyoyin bunkasa kasuwancinsu.

Hakan ya sa dillalai suka rage farashi, domin jan hankalin masu saye, lamarin da ya shafi yawan ribar da ake sa ran samu.

Wani masani ya ce yawan ribar da ake sa ran samu zai ci gaba da raguwa a fannin, saboda haka Samsung na bukatar rage kudaden da ya ke kashe wa, saboda ya cigaba da bunkasa.