Fari na barazana ga miliyoyin 'yan Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Miliyoyin 'yan Syria na bukatar agaji

Majalisar dinkin duniya ta yi kashedin cewa, fari na yin barazana ga rayuwar miliyoyin jama'ar kasar Syria.

Hukumar samar da abinci ta duniya-WFP ta ce, akwai karancin ruwan sama tun daga watan Samtuba, kuma hakan tasa amfanin gonar da ake sa ran samu bana ba zai taka kara ya karya ba:

Rahotanni sun ce yanzu haka dai mutane fiye da mutane miliyan tara ne ke bukatar tallafin gaggawa a Syria.

Yayin da rikicin kasar yake cigaba, ana kuma sa ran yawan mutanen dake bukatar dauki zai karu sosai.

A halin yanzu kuma hukumar ta WFP wacce ke samar da abinci ga miliyoyin 'yan Syria, ta ce ta rage yawon kason abincin da take baiwa mutane saboda karancin masu bata tallafin kudi.

Karin bayani