Rikici tsakanin Hausawa da Jukun a Taraba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An shafe kwanaki hudu ana aiki da dokar hana fita ba dare ba rana a Ibi dake jihar Taraba bayan rikicin Fulani da Tiv

Rahotanni daga Jihar Taraba dake arewacin Nigeria sun nuna cewar an yi tashin hankali tsakanin kabilar Jukun da Hausawa a kauyen Jubu dake karamar hukumar Wukari.

Rahotannin da muka samu sun nuna cewa a safiyar ranar Talata ne, aka samu tashin hankalin amma babu cikakkun bayanai game da rikicin.

Kabilar Jukun da ta Hausawa sun dade suna zaman tankiya a tsakaninsu, inda a wasu lokutan rikici tsakaninsu kan janyo hasarar rayuka.

Kawo yanzu jami'an tsaro ba su yi wani karin haske ba game da rikicin na kauyen Jubu.

Karin bayani