Sojoji sun musanta kashe Musulmi a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Nigeria

Rundunar tsaron Nigeria ta musanta zargin kashe Musulmi a kasar wadanda ba suji ba gani ba, inda ta ce zargin zai iya tada hankali.

Kakakin rundunar tsaron kasar, Manjo Janar Chris Olukolade a cikin sanarwar, ya ce dakarun kasar ba sa kashe mutane babu gaira babu dalili kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da son zuciya ba.

Kuma a cewarsa za ta ci gaba da ayyukanta na kawar duk wani abu da zai kawo barazana ga tsaron Nigeria.

Kungiyar Jama'atul Nasril Islam-JNI ce dai ta zargi sojojin kasar da kashe Musulmi babu gaira babu dalili a wani matakin da tace tamkar kokarin kawar da musulmin kasar ne.

Sakatare Janar na kungiyar Dr Khalid Aliyu a wata sanarwa, ya zargi jami'an tsaron da kashe Musulmi a jihohin Nassarawa da Yobe da kuma Borno, inda ya bayyana cewar ana neman a kawar da al'ummar musulmi a cikin kasar.

Karin bayani