'Za a yi zabe a Borno da Yobe da Adamawa'

Image caption Shugaban hukumar zaben Nigeria, Attahiru Jega

Hukumar Zaben Nigeria-INEC ta ce za ta gudanar da zabe a jihohin Borno da Yobe da Adamawa wadanda ke karkashin dokar ta-baci.

Shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega a hirarsa da BBC, ya bayyana cewar matsalar tsaro babbar kalubale ce ga gudanar da zabe, amma kuma za su yi iyaka kokarinsu don ganin cewar an yi zabe a daukacin kasar.

A watannin baya, an bayyana fargabar cewar barazanar tsaro a jihohi uku na arewa maso gabashin Nigeria saboda hare-haren 'yan Boko Haram ka iya janyo cikas a zabukan 2015.

Farfesa Jega kuma ya ce hukumar na kokarin sabunta rijistar zabe don gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2015.

Shugaban INEC din ya kara da cewar sun soma tantance jami'an zabe don tabbatar kaucewa magudi da aringizon kuri'u.

Karin bayani