An fara shirin aikin hajji a Nigeria

Miliyoyin musulmi ne ke zuwa aikin hajji duk shekara Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar ta ce tuni ta ba jihohi kujeru kuma ta fara maganar gidajen mahajjata a Saudiyya

A wani bangare na fara shirye-shiryen aikin hajji mai zuwa, hukumar aikin hajji ta Nigeria ta yi wani taro da nufin magance matsalolin da ake fuskanta duk shekara.

Taron na kwanaki biyu da aka yi a jihar Kano dake arewacin kasar, ya tattaro ma'aikatan hukumomin aikin hajji daga dukkan jihohin kasar.

Hukumar ta kasa ta jaddada muhimmancin fadakar da mahajjata, kan aikin hajji da tarbiyya da kuma bin dokokin Saudiyya.

Karancin kujeru dubu 19 da kasar ta samu a bara, yasa ta bullo da tsarin ba wa mahajjatan da basu taba zuwa ba fifiko.