Pistorius ya shafe da kuka a kotu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Oscar Pistorius

Mai gabatar da kara na gwamnatin Afrika ta Kudu, ya fara yin tambayoyi ga dan wasan tseren nan, Oscar Pistorius.

Daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali shi ne yadda ya nuna hotunan irin munanan raunukan da Reeva Steenkamp ta samu, lokacin da Mr Pistorius ya bude mata wuta bara.

Hankula sun tashi a kotun lokacin da mai gabatar da karar ya bukaci Mr Pistorius ya kalli hotunan.

Daga bisani sai da alkalin ta dage zaman kotun domin bada dama hankula su kwanta.

Shi dai Mr Pistorius ya musanta cewa da gangan ya harbe buduwar tasa yana cewa, ya zaci wani barawo ne.

Karin bayani