Radadin dokar ta baci a Taraba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A ranar Asabar da ta gabata ne aka sanya dokar hana fitar a Ibi

Rahotanni daga karamar hukumar Ibi dake jihar Taraba a Najeriya na cewa, kimanin mutane shida ne suka mutu sakamakon dokar hana fita ba dare ba rana.

Mazauna yankin sun tsinci kansu cikin wani mawuyacin hali, saboda cututtuka da rashin abinci da ruwan-sha ga kuma matsanancin zafi.

Kakakin gwamnatin jihar, Mista Kefas Sule ya ce rahoton yiwuwar samun wani tashin hankali, ya sa ba a sassauta dokar hana fitar ba, a ranar Talata.

Amma shugabannin 'yan sandan da na soji sun ziyarci yankin na Ibi, domin gane wa idonsu halin da ake ciki, kuma mai yiwuwa zuwa ranar Alhamis a sassauta dokar.