Amarya ta kashe Angonta da guba a Kano

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Wasila Umaru ta ce an yi mata auren dole

'Yan sanda a Jihar Kano da ke arewacin Nigeria sun tsare wata Amarya wacce ta kashe Angonta da wasu mutane uku ta hanyar dafa musu abinci da guba.

Wasila Umaru mai shekaru 14 ta yi amfani maganin bera wajen yi masa abinci saboda an yi mata auren dole.

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Kano, ASP Musa Magaji Majiya ya tabbatar da BBC tsare Wasila Umaru sannan ya ce bayaga mutane hudu da suka rasu, wasu mutane 10 suna asibiti saboda cin abincin.

A makon daya gabata ne aka yi auren, kuma Angon dan shekaru talatin da biyar ne.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana tuhumar Wasila Umaru da aikata kisan kai kuma idan an kamalla bincike za a gurfanar da ita gaban kuliya.

Karin bayani