Faransa ta yi kamen magungunan jabu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Faransa, Francois Hollande

Jami'an Kwastam a Faransa sun yi abun da suka kira kame mafi girma da aka taba yi a Tarayyar Turai na magungunan jabu daga China.

Kwalaben ruwan maganin jabu da za a yi wa mutane kusan miliyan biyu ne aka kama a tashar jiragen ruwa ta Le Havre dake Arewacin kasar ta Faransa.

Magungunan na cututtuka daban-daban ne da suka hada da gudawa da ciwon kai da kuma na kara karfin maza.

An boye magungunan ne a cikin wasu kwalaye da aka rubuta alamar Shayi a jikinsu.

Shugabannin Hukumar Kwastam ta Faransa sun ce magungunan da aka kama suna da hadarin gaske saboda ba su kunshi yawan sinadaran da ake bukata ba ko kuma ba su da ma sinadaran da ake bukata kwata-kwata.

Karin bayani