Ana zaben 'yan majalisar dokokin Indiya

Image caption An raba zaben Indiya zuwa gida tara

Mutane kimanin miliyan dari ne ke jefa kuri'a a ranar Alhamis, a sassa daban-daban na kasar Indiya domin zabar 'yan majalisa 91.

Ana zaben ne a jihohi 14, ciki har da jihar da tafi kowace yawan jama'a a kasar, wato Uttar Pradesh da kuma babban birnin kasar Delhi.

Masu zabe sun fito cike da zumudin jefa kuri'arsu a jihar Uttar Pradesh, wacce ke tura adadi mafi yawa na 'yan majalisa zuwa majalisar kasar.

Jam'iyyar Congress mai mulki na fuskantar kalubale daga jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta addinin Hindu.

Karin bayani