Gudun hijira: 'Nijar ba ta samu taimako ba'

'yan gudun hijira a Nijar
Image caption 'Yan gudun hijirar sun fito ne daga kasashen Mali da Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da karancin taimako daga kasashen duniya ga jamhuriyyar Nijar, da ke ba da mafaka ga 'yan gudun hijira 100,000.

Lamarin da Majalisar ta ce na janyo barazanar karancin abinci ga miliyoyin 'yan Nijar, bugu da kari ga fari da ambaliyar ruwa da kasar ta samu a 2013.

A watan Fabrairu ne dai Nijar da kawayenta suka nemi taimakon kudin euro miliyan 300 daga kasashen duniya, domin yaki da karancin abinci da tamowa da kuma taimaka wa 'yan gudun hijira.

Kimanin kashi biyu cikin dari na kudaden ne kawai suka zo hannu a karshen watan Maris, idan aka kwatanta da kashi 16 cikin dari da aka samu a daidai irin wannan lokaci a shekarar 2013.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba