'Ka da Jonathan ya tsawaita dokar ta-baci'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An girke jami'an tsaro a jihohin da ke karkashin dokar ta-baci

Gwamnoni uku na arewa maso gabashin Nigeria wadanda jihohinsu ke karkashin dokar ta-baci sun ce duk wani yinkurin tsawaita dokar bai dace ba.

A ranar 19 ga watan Afrilu ne dokar ta-baci da aka kafa a jihohin za ta kawo karshe a hukumance.

Gwamnonin su ne Murtala Nyako na Adamawa da Kashim Shettima na Borno da kuma Ibrahim Geidam na jihar Yobe.

Masu magana da yawun gwamnonin uku a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, sun ce babu wani sauran dalili da zai sa a kara tsawaita dokar ta-bacin.

Kawo yanzu dai gwamnatin Nigeria ba ta ce za ta kara tsawaita dokar ba, ko kuma za ta janye dokar a jihohin Adamawa da Yobe da kuma Borno.

Sanarwar ta hadin gwiwar kuma ta bukaci hukumar zaben kasar INEC ta yi koyi da takwaratta ta kasar Afghanistan wajen gudanar da zabuka a yankunan da ake fuskantar matsalolin tsaro.

Shugaban hukumar zaben Nigeria, INEC Farfesa Attahiru Jega ya jaddada cewar za su gudanar da zabe a daukacin kasar a shekara mai zuwa.

Kungiyar Boko Haram wacce ke da sansaninta a shiyyar arewa maso gabashin Nigeria ta hallaka dubban mutane a hare-haren da take kaiwa, sannan lamarin ya raba wasu dubbai da muhallansu.

Karin bayani