Yarjejeniyar zaman lafiya a Kudancin Kaduna

Image caption Dubban mutane sun rasa muhallansu saboda rikici a Kudancin Kaduna

Al'ummomin da ke zaune a Kudancin Kaduna dake arewacin Nigeria sun sanya hannu a kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a yankin.

Al'ummar Fulani da kuma wasu kabilu a kudancin jihar Kaduna suna rikici tsakaninsu a kan batutuwan da suka shafi addinni da kabilanci da kuma gona.

Sanya hannu a yarjejeniyar ya biyo bayan tattaunawar sulhu ta kwanaki biyu da aka yi karkashin wani kwamiti da Sufeto Janar na 'yan sandan kasar a wani kokarin kawo karshen rikicin dake tsakanin Fulani da Manoma.

Ko a cikin watan da ya wuce ma, an samu tashin hankali a karamar hukumar Kaura dake kudancin Kaduna inda mutane fiye da 100 suka rasu.

Jihar Kaduna na da kabilu da dama musamman a yankin kudanci wadanda galibinsu Kirista ne kuma suna zaman doya da manja da Fulani wadanda galibinsu Musulmi ne.

Karin bayani