Majalisar Dinkin duniya za ta tura soji CAR

Kwamitin Tsaro Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kwamitin Tsaro

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuriar amincewa da tura sojojin kiyaye zaman lafiya dubu goma sha biyu zuwa Jumhuriyar Tsakiyar Afrika.

A halin yanzu dai, dakarun kiyaye zaman lafiya dubu shidda ne na Tarayyar Afrika da dubu biyu na Faransa suke kokarin maido da doka da oda a kasar, yayin da ake cigaba da tashin hankali tsakanin kungiyoyin sa-kai na Musulmi da na Kirista masu dauke da makamai.

Ministan harkokin wajen kasar ta Jumhuriyar Tsakiyar Afruka, Toussaint Kongo-Doudou, ya ce matakin amincewa da kudurin, mafari ne na wani muhimnin shiri da zai share fagen hanyar warware rikicin da kasarsa ke fama da shi.

Sai dai an soki lamirin Majalisar Dinkin Duniyar bisa jinkirin da aka samu wajen daukar matakin.