Kwarin gwiwa wajen gano jirgin Malaysia

Iyalan wadanda ke jirgin Malaysia Hakkin mallakar hoto
Image caption Har yanzu iyana wadanda suke cikin jirhin ba su daina jimamai ba, tare da sa ran za a gano wani abu daga cikin jirgin.

Prime Mnistan Australia Tony Abbot yace yana da kwarin gwiwar cewa alamomin da ake ji na rukodar nadar bayanan jirgin Malaysian nan ne da ya bata.

Ya kuma ce an rage fadin yankin da ake bincike a cikinsa sosai, an rage fadin sosai ne saboda ana da jerin saututtukan da aka jiyo na tsahon lokaci.

A yanzu an kusa isa inda ake jiyo sautin da muke da kwarin gwiwar na rikodar jirgin ne, tare da sa ran samun bayanan isassu kafin batirin rikodr ya mutu.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a kasar Sin, ya ce alamomin da ake ji akai-akai a 'yan kwanakin nan ya bawa masu aikin binciken damar sake fadada binciken nasu a a cikin tekun India.

Tony Abbot ya kara da cewa ayayin da batirin rukodar ke gab da mutuwa, masu aikin binciken na kokarin samu bayanai tun kafin lokaci ya kure musu.

Karin bayani