Cutar kwalara ta barke a Bauchi

Image caption Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda

Cutar kwalara ta barke a Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Nigeria inda ta hallaka mutane kusan 60 tun daga farkon wannan shekarar.

Bayanai sun nuna cewar kawo yanzu mutane kusan 1,000 sun kamu da cutar inda su ke karbar magani.

Gwamnatin jihar ta Bauchi ta ce galibin wadanda cutar ta kama almajirai ne.

A duk shekara a Nigeria ana samun barkewar cutar kwalara sakamakon gurbataccen ruwan sha da kuma abinci.

Mutane a yankunan karkara a Nigeria na fuskantar karancin tsabtataccen ruwan sha da kuma muhalli abinda ke kara janyo muni idan cutar ta bulla.

Karin bayani