Macizai sun addabi jama'a a Gombe

Image caption Nigeria na da kwararrun cibiyoyin jinyar masu sarar maciji uku a Gombe da Taraba da Plateau

A Najeriya ana samun karuwar mutanen da ke gamuwa da sarar macizai, musamman a jihar Gombe, inda yawansu ya kai kusan 400 a wata.

Hakan ya biyo bayan yanayin zafi da ake ciki, abin da ke sa macizan fitowa daga maboyarsu, sannan mutane kuma na kwana a waje.

Bugu da kari saboda a lokacin damuna manoma na yawan shiga daji, abin da ya sa likitoci ke bada shawarar yin taka-tsantsa, domin kiyaye wa.

Sai dai daya daga cikin manyan asibitocin da ke kula da masu fama da sarar maciji a garin Kaltungo cikin jihar Gombe, na fama da matsalar karancin gadajen kwanciya da kuma wutar lantarki.