Batun kudaden taron Najeriya

Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar dai shi ya fara bude taron da jawabinsa, inda daga bisani ya bar mahalarta taron suka ci gaba tafka mahawara akan batutuwan da ya bude taron da su.

A Najeriya, mahalarta babban Taron kasa sun kammala jin ra'ayoyin wakilan taron dangane da jawabin da Shugaban Kasar ya gabatar musu.

An dai shafe makonni biyu ana tattaunawa kan jawabin Shugaba Goodluck Jonathan inda wakilan daya bayan daya su ka yi ta sharhi iri-iri akan jawabin shugaban kasar.

Galibin wakilan dai yabawa suke yi game da abubuwan da jawabin ya kunsa, inda kuma suka tattauna dimbin matsalolin dake ciwa kasar Tuwo a kwarya da kuma bada shawarwari kan yadda za'a magance matsalolin.

Sai dai kamar daya daga cikin batutuwan da suka taso yayin tattaunawar shine kudaden da ake baiwa wakilan.

Inda mahalarta taron ke cewa wasu jaridun na yada jita-jitar yawan kudaden da aka basu alhalin ba hakan ba ne.