Ukraine na kokarin shawo kan masu fafutuka

Masu goyon bayan Rasha a Ukraine na bore Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ukraine ta ce za ta yi amfani da karfi, idan ta kama a gabashin kasar

Firai Ministan Ukraine na wucin-gadi, Arseniy Yatsenyuk ya shaida wa jami'ai a Donetsk cewa, zai karawa hukumomin yankuna karfin iko.

Haka kuma ya ce Rashanci zai cigaba da zama harshen da ake amfani da shi a gabashin kasar.

Masu fafutuka da ke goyon bayan Rasha na cigaba da mamaye gine-ginen gwamnati a yankin, inda suke neman cin gashin kansu ko kuma hade wa da Rasha.

Rashar ta musanta zargin da Ukraine da kasshen yammacin duniya ke yi mata, na cewa ita ce ke ingiza wutar rikicin Ukraine din.