Cacar baki tsakanin Nigeria da Zimbabwe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe

Nigeria ta gayyaci wani jami'in diplomasiyyar Zimbabwe a kasar ta don yayi bayani a kan kalaman da Shugaba Robert Mugabe ya yi a kan cin hanci da rashawa a Najeriyar.

A watan Maris ne Shugaba Mugabe ya ce 'yan kasar sa sun fara zama kamar 'yan Najeriya, wadanda sai sun bada na goro kafin su samu biyan bukata.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta bayyanawa jami'in Zimbabwen cewa ba za ta amince da irin wannan caccakar ba, da ka iya zubar mata da mutunci.

Jadawali kan cin hanci da rashawa a duniya da kungiyar Transparency International ta fitar, ya nuna cewar cin da hanci yafi muni a kasar Zimbabwe idan aka kwatanta da Nigeria.

Karin bayani