Ana cin zarafin mata a Nijar

Shugaba Muhammadou Issoufou na jamhurijar Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana dai son a hukunta masu aikata laifin hukunci mai tsauri.

Masu fafutukar kare hakki yara a jamhuriyar Nijar sun ce ana samun karuwar yi wa yara 'yan mata cikin a birni na biyu mafi girma a kasar wato Maradi.

Hukumomi a jahar ta Maradi dai sun ce wannan matsala ta yi kamari sosai a daidai lokacinda ake nuna damuwa da rashin dokokin hukunta mazajen da ake kamawa da wannan laifi yiwa 'yan matan ciki.

kungiyoyin dai sun ce iyayen yaran na taka muhimmiyar rawa wajen aukuwar lamarin.

Ta yadda ba sa sanya idanu akan shige da ficen 'ya'yansu, haka kuma sun bukaci da ayi dokar da zata hukunta duk wanda aak samu da aikata laifin.

kuma hukunci mai tsauri.