Iyalan Ba'are Mainasara sun shigar da kara

Image caption Bazoum Muhammed shi ne ministan harkokin wajen Nijar.

Iyalan tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar da aka kashe a cikin wani juyin mulki shekaru 15 da suka wuce, wato Marigayi Ibrahim Ba'are Mainasara sun kai gwamnatin kasar kara gaban kotun kasa da kasa ta kungiyar ECOWAS.

Iyalan dai na neman kotun da ta tabbatar da cewa kasar ta Nijar ce ke da alhakin kisan da aka yi masa saboda an kashe shi ne da makamin da gwamnatin kasar ta saya don kare al'ummarta.

Haka ma iyalan tsohon Shugaban na neman kotun da tilastawa kasar ta Nijar zakulo wadanda suka aikata kisan.

''Mun gane tsawon shekaru 15 a nan Nijar ko 'ina suka yi kara sai a yi watsi da karar tasu, shi yasa muka kai wannan karar gaban kotun kasa da kasa ta Ecowas'' inji lauyan iyalan Chaaibou Abdourrahmane.

Karin bayani