Ana tuhumar jariri da yunkurin kisa

Musa Khan da ake zargi da hannu a yunkurin kisan dan sanda Hakkin mallakar hoto GEO TV
Image caption Jaririn dai na rike da bulunbotin madararsa, a lokacin da ake shugar da karar zargin da ake masa shi da iyayensa, kana aka kuma yi amfani da tambarin yatsunsa.

A yau ne kotun Pakistan da take tuhumar jaririn nan dan watanni tara da iyayensa da zargin yunkurin kisan kai a makon da ya gabata, zata fara sauraren kara.

Duk da karancin shekarunsa an tafi da Musa Khan da iyayensa kotu da ke Lahore, tare da tuhumarsu da yunkurin kashe wani dan sanda.

A lokacin wata taho mu gama kan biyan kudin wutar lantarki da iskar Gas.

Wakilin BBC ya ce dan jaririn mai suna Musa Khan ya dai zama abin kallo ba a pakistan kadai ba har ma da kasashe makota a lokacin da ya bayyana a gaban kotu.

An kuma yi amfani da tambarin hannunsa a lokacin shigar da karar,ya yin da daya hannun ke rike da bulonbotin madararsa.

Sai dai an bada belin jaririn, ya yin da manyan jami'an 'yan sanda suka ce kar a kara tuhumarsa da laifin.

Sun kuma bada damar hukunta dan sanda da ke gudanar da bincike kan lamarin.