An kwace hedikwatar 'yan sanda a Ukraine

'Yan bindigar da suka kwace hedkwatar 'yan sanda a Ukraine.  Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan bindigar da suka kwace hedkwatar 'yan sanda a Ukraine

Wasu 'yan bindiga, sanye da kayan soja da ba a tantance ko su wane ne ba, sun kame hedikwatar 'yan sanda a birnin Slaviansk na kasar Ukraine.

Wani kakakin 'yan sanda Ihor Dyomin ya shaidawa gidan telbijin na kasar cewa 'yan bindigar sun zo ne dauke da muggan makamai.

Yace ya zuwa yanzu dai ba su fadi bukatunsu ba. Yana cewar suna kokarin sanin manufarsu. Yace adadinsu zai kai 15 zuwa 20; yana mai cewa sun kame ginin ba tare da wata-wata ba, bayan sun yi amfani da borkonon-tsohuwa.

Ministan cikin gidan kasar na wucin gadi, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za a dauki matakan ba-sa-ni ba-sa-bo a kan mutanen.

Karin bayani