Dangantakar Iran da Amurka ta kara sukurkucewa

  • 12 Aprilu 2014
Shugaban Iran Hassan Rouhani Image copyright Reuters
Image caption Shugaban Iran Hassan Rouhani

Mataimakain Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce kasar sa ba ta tunanin nada wani jakada zuwa hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake Amurka, don maye gurbin Hamid Abutalebi da Amurkar ta hanawa Iznin shiga kasar ta.

Abbas Araqchi ya ce za su yi amfani da hanyar shari'a don kalublantar shawarar Amurka ta hana Abuteleb din Visa.

Ana danganta Abutelib da kungiyar da ta kame ofishin jakadancin Amurka a Tehran a shekarar 1979, kuma wasu da dama a Amurkar na nuna adawa da nadinsa.

Karin bayani