Amurka ta hana jakadan Iran iznin shigarta

Hakkin mallakar hoto ISNA
Image caption Mr. Abutalebi dai ya ce baya daga cikin gungun daliban.

Fadar Gwamnatin Amurka ta White House ta ce kasar ba za ta ba mutumin da Iran ta ba da sunansa a zaman sabon jakadanta zuwa Majalisar Dinkin Duniya mai hedikwata a birnin New York iznin shiga kasar ba.

Amurka na zargin Hamid Abutalibi ne da zama daya daga cikin gungun daliban da suka afkawa ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Tehran a 1979, kuma Amurka na matukar adawa da ba shi mukamin.

Iran dai ta kira matakin na Amurka a zaman abin kaito wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.

An yi imanin cewar Amurka ba ta taba hana wa wani jakada zuwa Majalisar Dinkin Duniya iznin shiga kasar ba, amma masu aiko da rahotanni sun ce akwai damuwa a tsakanin jami'an diplomasiyya kan kofar da yin hakan yanzu zai bude.

Karin bayani