An kashe mutane 38 a Jihar Borno

Wasu 'yan bindiga wadanda ake kyautata zaton cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane 38 a wasu tagwayen hare-hare da su ka kai a Jihar Borno, arewacin Najeriya.

Haka kuma sun kone gidaje da dama a hare-haren, wadanda su ka kai a garin N'Goshe-Sama da kuma Kaigamari a ranakun Asabar da Lahadi.

Wani mazaunin garin N'Goshe-Saman, wanda ya tsira daga harin, ya sheda wa BBC cewa 'yan bindigar sun rika bi gida-gida, suna kashe mutane, suna kuma cinna wa gidajen wuta.

Ga cewarsa, kimanin mutane 30 ne aka kashe a N'Goshe-Sama.

Ya ce an fara harbe harbe ne tun karfe goma na daren Asabar har zuwa ran Lahadi da safe.

Ya kuma ce babu wani dauki da jami'an tsaro su ka kaima masu.

An kai harin na biyu ne a kauyen Kaigamari inda aka kashe kimanin mutane takwas, ga cewa wani mazaunin wurin.

Ya ce mutane na zaman fargaba sosai yanzu a kauyen.

Jami'an tsaro dai ba su komai ba akan wadannan hare haren.

Yakar 'yan ta'adda

Sai dai a wata sanarwar da ta bayar ranar Lahadi, rundunar sojin kasar ta ce ta na ci gaba da yakar wadanda ta kira 'yan ta'adda a yankin arewa-maso-gabacin kasar.

Ta kuma yi ikirarin cewa ta na samun nasara akan su.

Ta kuma ce ta farma sansanonin wasu 'yan bindiga a jihohin Kaduna da Plateau, inda ta ce ta kama makamai da kuma shanu wadanda ake zargin cewa na sata ne.

Karin bayani