Ukraine na 'kokarin kawadda 'yan ta'adda'

Hakkin mallakar hoto AP

Ministan cikin gida na wucin gadi a Ukraine, Arsen Avakov, yace yanzu haka dakarun su na kokarin kawadda wadanda ya kira 'yan tada'adda, a birnin Slaviansk na gabashin kasar.

Wasu, sanye da kayan soja ne suka kame wani ofishin 'yan sanda da sauran gine-ginen hukuma a birnin.

Ministan yace an hallaka wani jami'in tsaron kasar, kuma wasu damama sun samu raunuka daga bangarorin biyu.

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO yace ya damu matuka, a bisa abunda ya kira wani yunkuri na jefa Ukraine cikin rudani.