Mun soma yaki da ta'addanci -Ukraine

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magajin garin birnin Slaviansk ya ce maharan na neman a yi kuri'ar raba-gardama ne.

Gwamnatin Ukraine ta ce jami'an tsaron kasar sun fara ''yaki da ta'addanci'' a birnin Slaviansk da ke gabascin kasar; inda wasu 'yan bindiga suka kwace iko da ofisoshin 'yansanda da na jami'an leken asiri ranar Assabar.

Ministan harkokin wajen kasar, Arsen Avakov ya ce harin, aikin cin zali ne daga Rasha.

Wannan matakin dai ya biyo bayan da Amurka ta bayyana damuwa kan rikicin wanda ta kira hare-hare wadanda aka riga aka tsara da 'yan aware masu goyon bayan Rasha suka kai.

Amma Kamfanin Dillancin Labaran Rasha, Itar-tass, ya ambato ministan harkokin wajen Rasha Sergei Levrov na cewa rikicin da Ukraine ke ciki, na faruwa ne saboda kasawar gwamnatin kasar ta biyan halattattun bukatun al'ummar kasar da ke magana da harshen Rashanci.

Karin bayani