Bom ya hallaka mutane 24 a Nyanya Abuja

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lamarin ya shafi motoci kusan talatin

Wani abu da ake zaton bom ne ya fashe a tashar motoci dake Nyanya a Abuja babban birnin Nigeria, inda bayanai suka nuna cewar mutane da dama sun rasu.

Wata majiya a hukumar agajin gaggawa a Nigeria ta bayyana cewar kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 24 a yayinda wasu 62 suka samu raunuka, sai dai har yanzu ba a gama kirga adadin wadanda suka rasu ba.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da mutane ke kokarin tafiya wurin aiki.

Wani da ya gane wa idanunsa abin da ya faru ya shaida wa BBC cewa mutane da dama sun rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata.

Wasu kafafen yada labarai sun ce motoci akalla 30 ne suka kone sakamakon afkuwar lamarin.

Wakilin BBC da ya ziyarci daya daga cikin asibitin da aka kai gawarwaki ya tattauna da wasu mutane da dama sun rasu.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tuni ma'aikatan ta suka isa wajen suna kwashe gawawwaki tare da garzaya wa da wadanda suka ji rauni asibiti.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu aikin gaggawa na kokarin aikin ceto

Karin bayani