Nyanya: Birtaniya ta nuna alhini ga Nigeria

Sakataren harkokin wajen Birtaniya

Sakataren Harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya bayyana takaicinsa game da harin bama-baman da aka kai a Nyanya dake gabashin Abuja.

Inda ya yi tur ga wanda ke da alhakin harin, yana mai fatan za a hukunta su nan ba da dadewa ba.

"Ina mika ta'aziyyar gwamnatin Birtaniya ga iyalan wadanda suka mutu da kuma wadanda suka samu raunuka."

"Za mu cigaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin Najeriya, domin taimaka mata wajen magance barazanar da take fuskanta na ta'addanci."

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba