Jirgi marar matuki na laluben jirgin Malaysia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin Malaysia ya yi layar zana

A karon farko za a tura wani jirgi marar matuki, mai tafiya a karkashin teku, a cigaba da binciken da ake na gano jirgin saman Malaysia da ya bata.

Jirgin zai shiga yin bincike a can karkashin tekun India, nesa da gabar ruwan Australia daga yamma, inda ake tsammanin an ji signa daga na'urar nadar bayyanan jirgin saman.

Jami'in Australia mai kula da aikin neman jirgin ya ce, watakila a yanzu baturan na'urar nadar bayyanan sun daina aiki.

Ya kuma kara da cewa, an gano man da ya kwarara a yankin da ake gudanar da binciken.

To amma za a iya daukar kwanaki kamin a san ko man jirgin saman da ya batan ne.

Karin bayani