Google zai sayar da gilashin Fasaha

Gilashin fasaha na Google Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Google zai sayar da gilashin ne ga duk wanda ya fara bukata

Za a sayar da gilashin fasaha na Google ga jama'a a Amurka a ranar Talata 15 ga watan Maris, kamar yadda kamfanin ya sanar.

Wadanda za su amfani da shi dole su zamanto sun kai shekaru 18 a duniya, kuma sai sun cike wata takarda a intanet, domin yin odar gilashin kafin a sayar musu.

kudin gilashin dai dala 1,500, kuma wadanda za su hada gilashin a Burtaniya za su fara samunsa nan da farkon watan Mayu.

Tsadar gilashin zai sanya wasu masu dokin zuwansa, za su jira sai farashin ya sauka.

A shekarar 2013 an sayar da gilashin ga mutane 8,000, a bangaren wani shiri na kamfanin na gwajin kasuwa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Google zai sayar da gilashin ne ga duk wanda ya fara bukata

A yanzu kamfanin zai bai wa mutane da yawa damar gwada kwamfutar, alamun dake nuni da cewa, kamfanin na gab da shigar da gilashin kasuwa.

Tawagar dake aiki kan gilashin ta ce "Mun kagu mu samu wasu wadanda za su yi amfani da gilashin, kuma muna jiran tsokacinku game da shi."

Google na son gilashin ya shiga hannu wasu karin mutane, domin gano yadda za su kara inganta shi, saboda haka ba sa son masu matsakaitan masu amfani, har sai sun kammala gyara shi.

Sai dai wasu na ganin kudin gilashin ya yi tsada, ganin ayyukan da zai iya yi takaitattu ne.