An kama 'yan kasuwar Somalia 20 a Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai miliyon 'yan gudun hijirar Somalia a kasar Kenya

'Yan sanda a Kenya suna binciken 'yan kasuwa 20 wadanda ake zargin suna baiwa kungiyar Al-Shabab ta Somalia tallafin kudi.

Wannan shi ne matakin baya-bayannan da jami'an tsaro su ka gudanar inda suka damke mutane fiye da 4,000 galibin 'yan Somalia.

'Yan sanda sun ce suna nazarin asusun ajiyan mutanen da kuma musayar kudaden kasashen waje a matsayin hanyoyin baiwa kungiyar tallafin.

'Yan kasuwa a Kenya 'yan asalin Somalia sun zargi gwamnatin Kenya da kokarin durkusar dasu.

Kungiyar Al-Shabab ta Somalia ta kai hare-hare a Kenya.

Karin bayani