An soma shari'ar Saif al-Islam a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saif al-Islam Kaddafi

An soma shari'ar Saif al-Islam, dan tsohon Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi da aka hambarar.

Ana tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa da kuma aikata laifukan yaki.

Ana tuhumarsa tare da wasu karin manyan jami'an tsohuwar gwamnatin ta Libya.

Saif al-Islam bai halarci zaman kotun ba, amma sauran wadanda ake tuhumarsu tare wato Abdullah al-Senussi da kuma tsohon Firaminista Baghdadi al-Mahmoudi sun bayyana gaban kuliya.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC na zargin Saif al-Islam da aikata laifukan yaki a lokacin boren da aka kifar da gwamnatin mahaifinsa.