'Yan bindiga sun yi yunkurin sace nakiyoyi

'Dan sandan Nigeria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mahara sun sha satar makamai daga 'yan sanda bayan sun kai musu hari

'Yan bindiga sun sace dumbin sinadaran hada nakiyoyi da kuma wayoyin tayar da bama-bamai ko nakiyoyi daga kamfanin Mother Cat a jihar Bauchi.

Lamarin ya faru ne a garin Yana dake karamar hukumar shira a ranar Litinin da safe.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce jami'an tsaro sun yi musayar wuta da 'yan bindigar, abin da ya sa suka gudu suka bar ladansu.

Kuma sun ce sun gano dimbin albarusai da kuma abubuwa masu fashewar da 'yan bindigar suka sace a motar da suka bari.