Boko Haram: An sace dalibai mata 100

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu dalibai da 'yan Boko Haram su ka sace

Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram sun kai hari a kan wata makarantar mata, inda suka yi awon gaba da dalibai da dama.

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda ta ce dalibai mata sama da100 ne aka sace.

Wasu mazauna garin sun ce 'yan Boko Haram sun kaiwa makarantar hari ne a cikin daren ranar Litinin.

Bayanai kuma sun nuna an kona gidaje da dama a garin na Chibok

Ko da yake wasu iyaye da BBC ta yi hira da su, sun ce kawo yanzu basu ga 'ya'yansu ba, yayin da wasu 'yan matan kalilan suka samu kubucewa.

Jihar Borno ce matattarar kungiyar Boko Haram, inda suka kashe mutane fiye da 1,800 a wannan shekarar.

Hakan na zuwa ne bayan wani hari da aka kai Nyanya dake wajen garin Abuja, inda aka kashe mutane 72 tare da raunata mutane fiye da 130.

Karin bayani