'Mutane 1000 sun mutu a rikicin kabilanci'

Taswirar Nigeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan gudun hijirar rikicin Benue na zaune a sansanoni shida dake Makurdi

Karuwar tashin hankali a jihohi biyar dake tsakiyar Nigeria ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 1,000 tun daga watan Disambar bara.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ce ta bayyana hakan, inda ta kara da cewa gazawar hukumomin Nigeria wajen biciken hare-hare tare da hukunta masu laifi zai iya ta'azzara yanayin.

Hukumar ta kuma ce tashin hankalin wanda rikici tsakanin Fulani da manoma dake iza wutar rikicin shekara da shekaru, na iya bazuwa wasu jihohin arewacin kasar.

Jihohin da rikicin ya shafa a cewar hukumar sun hada da Nasarawa da Benue da Taraba da kuma Plateau da Kaduna, yayin da tashin hankalin ke bazuwa cikin Zamfara da Katsina.