An kashe matafiya 18 a Gwoza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun tsaro na sintiri a Borno

Rahotanni daga garin Gwoza dake jihar Borno a arewacin Nigeria sun ce wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe matafiya akalla 18.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata.

Wani mutumi da ya kubuta ya bayyana cewar maharan na sanye ne da kayan sojoji.

Bayanai sun nuna cewar ana samun karuwar kai hare-hare a jihar Borno duk da cewar kasar na karkashin ikon dokar ta baci.

A cikin makon daya gabata ma an kashe mutane fiye da 100 a garuruwa daban daban na jihar ta Borno.

Karin bayani