Nigeria: Ana so mutane su taimaka da jini

Harin bom a tashar Nyanya Abuja Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harin bom a tashar Nyanya Abuja Najeriya

Mutane da dama da suka jikkata a harin bam a tashar Nyanya dake wajen birnin tarayyar Abuja, na matukar bukatar a yi masu karin jini.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya , NEMA ta yi kira ga al'umma da su je asibitoci, domin bayar da gudunmawar jini ga jama'ar da wannan hari ya rutsa da su.

Mutane akalla 71 ne dai suka rasu, sakamakon fashewar bama-baman.

Shugaba Jonathan ya ziyarci inda lamarin ya faru kuma ya yi tir da harin, tare da dora alhaki kan kungiyar Boko Haram.