Helikwabtocin soji sun kai dakaru kudancin Sloviansk

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu goyon bayan Rasha na taba kayar baya

Shugaban Ukraine na riko, Olexander Turchynov, ya ce dakarun kasar sun sake karbe wani sansanin mayakan sama da ke gabashin kasar, bayan sun gwabza da 'yan aware masu goyon bayan Rasha.

Wani wakilin BBC a wajen ya ji karar bindigogi, kuma kamar yadda ya ce, a yanzu wasu mazauna yankin, masu ra'ayin Rasha, a fusace sun killace sansanin sojan mai nisan kimanin kilomita sha biyar, a kudu da garin Sloviansk.

Wasu jiragen helikopta biyu na soja, sun kai dakaru zuwa sansanin mayakan saman.

Kuma motocin sulke dauke da bindigogi, sun taru a wani yanki mai nisan wajejen kilomita arba'in a arewa da Sloviansk.

Tun farko dai shugaban Ukraine na riko, Oleksander Turchynov, ya gaya wa majalisar dokokin kasar cewa, jami'an tsaro sun soma kai farmakin korar wasu 'yan bindiga, masu goyon bayan Rasha.

'

Karin bayani