'Yan Boko Haram sun kashe dagacin Gwoza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun addabi jama'a

'Yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe akalla mutane 18 a garin Gwoza na jihar Bornon arewacin Nigeria.

Daga cikin wadanda aka kashe harda dagacin garin na Gwoza.

Wani mazaunin garin ya shaidawa BBC cewar 'yan bindigar na sanye ne da kayayyakin sojoji.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da neman yaran 'yan mata na makarantar sakandare da 'yan Boko Haram suka sace a ranar Litinin.

An sace dalabai mata 129 a wata makarantar kwana da ke garin Chibok a kudancin jihar Borno.

Kawo yanzu wasu daga cikin 'yan matan sun kubuta daga hannunj 'yan Boko Haram.

Karin bayani