Kasuwar bayan fage ta Salula a London

Akwai kasuwar bayan fage, inda shaguna da 'yan kasuwa ke maraba da wayoyin komai da ruwanka na sata a London, kamar yadda BBC ta gano.

Bayanan sirri na nuna cewa wasu shaguna a Swathe da ke gabashin London na farin cikin sayen wayoyi salula daga hannun barayi.

An dauki hoton bidiyon wasu 'yan kasuwa biyu da ke sayen wayar Samsung S3 da iPhone 4 daga hannun wani mai bincike da ya yi shigar burtu, cewa shi barawo ne.

Duk da cewa ya fito karara ya nuna cewa wayoyin na sata ne.

Sai dai shagunan da abin ya shafa sun ki cewa komai game da batun.

An sace wayoyin komai da ruwanka fiye da 30,000 a shekarar 2013 a London.

'Yadda ta wakana'

Da samun labarin irin wannan cinikayyar, sai aka samu wayoyin komai da ruwanka da aka taba amfani da su ta halattacciyar hanya.

Sai aka sanya hotuna da lambobin mutane tare da aika sakonni a kowacce daga cikinsu.

Sai aka rufe layukan, ko kuma aka bada rahoton an sace wayoyin.

Mai binciken wanda ya yi shigar burtu sai ya je sayar da wayoyin, wanda a fuskarsu an rubuta "An sace wannan wayar ne, saboda haka an rufe layin, kuma an bada rahoto ga hukumomi."

Sai mai binciken ya kai waya daya wani shagu mai suna London Mobile Ltd a garin Ilford ya ce "Ba saya na zo ba, na sato ne"

A lokacin da aka nuna sakon dake fuskar wayar ga wani wanda yake aiki a shagon sai ya yi dariya yace "Ka sato ne hakan yana da hadari.

Fadin hakan bai hana shi karbar wayar ba, ya kuma bada kudi.

Wani shago dake kusa kuma Mobiles and Computers da ke Seven Kings ya sayi wayoyin "sata" hudu daga hannun BBC, kuma mai binciken ya bar shagon kafin su amince za su saya a kan kudi fam £40.

Hakan ya faru duk da cewa a komawarsa ta biyu, mai binciken ya ce "dan uwa na sake sato wasu karin biyu."

Wani ma'aikacin ma har lada ya baiwa mai binciken, saboda ba a kama shi ba.

Inda ya ce "Ba ka da hankali, ka kashe wayar idan ba haka ba za su iya gano ka."