Chibok: 'Yan mata 8 suka rage a hannun 'yan bindiga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Kashim Shettima

Hedikwatar rundunonin sojan Najeriya ta ce, sojoji sun yi nasarar kubutar da karin 'yan matan da aka sace a Chibok , tare da kama daya daga cikin 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

A cikin wata sanarwa, hedikwatar sojan ta bayyana cewar shugabar makarantar ta tabbatar da cewa yanzu 'yan maata 8 ne suka rage a hannun 'yan bindigar, kuma sojoji na ci gaba da kokarinsu na gano wadannan 'yan mata .

Tun farko Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya yi alkawarin bada tukwicin naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada bayanai game da 'yan matan sakandare da aka sace a jihar.

A ranar Litinin ne, 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata na makarantar sakandare ta kwana da ke garin Chibok su fiye da 100.

A cikin hirarsa da BBC, Gwamna Shettima ya ce matakin bada tukwicin zai taimaka wajen gano inda aka kai 'yan matan da aka sace.

Gwamnan ya nuna damuwa game da tabarbarewar tsaro a jihar, inda ya ce ko a lokacin yaki a Musulunci ba a taba yara da mata.

Alhaji Kashim Shettima ya ce daga cikin 'yan matan da aka sace guda 14 sun kubuta, a yayinda ya ce yana tuntubar shugaban makarantar ta Chibok da Hakimin garin domin samun bayanai game da inda aka kwana a aikin lalubo 'yan matan.

Rundunar sojin Nigeria ta ce tana aikin hadin gwiwa domin kokarin ceto 'yan mata.

Mutane fiye da 1,800 ne suka mutu a rikicin Boko Haram a wannan shekarar.

A ranar Litinin ma wani bam da ya tashi a wata tashar mota a Nyanya da ke Abuja ya janyo rasuwar mutane akalla 76 a yayinda fiye da 130 suka samu raunuka.

Karin bayani