Ana ceton fasinjojin jirgin Koriya ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tawagar masu ninkaya tare da jiragen ruwa 50 ne ke aikin ceton wadanda suka bace

Masu gadin Teku a Koriya ta Kudu sun ce kimanin fasinjoji kusan 300 ne ba a gansu ba, bayan wani jirgin ruwa na fito ya nutse.

Akasarin fasinjojin jirgin 459, 'yan babbar makaranta ne da suka je yawon-bude-ido a tsibirin Jeju.

Kafofin watsa labarai na Korea ta Kudu sun ce an ceto mutane sama da 150, daga kan jirgin fiton-wanda ruwa ya kusa cinye shi, an kuma tabbatar da mutuwar mutane biyu.

Amma ana cigaba da aikin ceto da jiragen ruwa masu yawa da kananan jiragen sama, masu saukar ungulu.