Mutane 47 sun rasu hadarin mota a Togo

Wata Motar Safa da babbar Motar dakon-kaya sun yi taho mu gama a kasar Togo inda suka hallaka akalla mutane 47 tare da jikkata wasu da dama.

Gidan talabijin na kasar ya ce hadarin ya faru ne cikin dare a ranar litinin, kuma akasarin mutanen da suka mutu 'yan kasar Togon ne, yayinda goma sha-biyar suka fito daga Burkina Faso da Nijeriya.

Mutanen da suka shaida lamarin sun ce babbar motar tana da idon fitila ne guda daya, don haka akwai tsammanin cewa babur ne ke tafiya ba wai Mota ba.

Motocin biyu dai sun yi karo ne a wani wuri mai nisan kimanin kilomita dari da saba'in da biyar a yankin arewa maso yammacin Lome babban birnin kasar.

Karin bayani